Spread the love

Buhari ya aikawa majalisa sabon Shugaban Hukumar Alhazai ta ƙasa da yake so naɗawa

Shugaba Muhammadu Buhari ya aika da sunan Zikrullah (Sikiru) Olakunle Hassan zuwa ga majalisar dattawa ta ƙasa domin tantance shi a matsayin sabon shugaban hukumar Alhazai ta ƙasa.

Ustaz Zikirullah, wanda dan asalin jihar Osun ne, zai maye gurbin Muhammad Mukthar ne a matsayin shugaban hukumar ta Alhazai bayan wa’adin sa ya cika, matuƙar majalisar ta amince da shi.

Takardar neman tabbatar da shi tana ɗauke da kwana 28 Nuwamba 2019, takardar mai taken naɗin shugaba da mambobin hukumar.

Shugaban majalisar dattawa Dakta Lawan Ahmad ya karanta sunayensu da suka haɗa da, kwamishinonin hukumar Abdullahi Magaji Harɗawa da Nura Hassan Yakassai da Shaikh Momo Suleiman Imonikhe.

Mambobin hukumar Abba Jatto da Garba Umar daga jihar Sokoto da Ibrshim Ogbonnia da Sagir Musa da sauransu.

Barista Abdullahi Mukhtar Muhammad ɗan jihar Kaduna ne tsohon shugaban ƙasa Jonathan ya naɗa shi matsayin da ya kammala wa’adinsa a yanzu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *