Spread the love

Ɗiyar Shugaban ƙasa Aisha M Buhari Jnr (Hanan) ta kammala digirinta na farko a Turai da kyakkyawan sakamako in da ta samu matakin farko a digiri (first class degree).

Uwar gidan shugaban ƙasa Hajiya Aisha Buhari ta godewa al’ummar jihar Kebbi kan karimcin da suka yi wa ‘yarta na goyon bayan da ta samu a gudanar da kundin bincikenta a jihar.

Ta kuma godiya ta musamman ga Gwamnan Kebbi Atiku Bagudu, da ƙanensa Ibrahim Bagudu, da Uwar gidan Gwamnan Kebbi da sarakunan Gwandu da Daura.
Ta yi fatan alheri ga sauran ɗalibai a rayuwarsu ta gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *