Spread the love

Maigirma Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya karɓi Kyautar Kambin da Jihar Sokoto ta ci a Wajen bukin E-Nigeria da ta zo ta 2 a wajen amfani da hanyoyin zamani na ICT a ayukkan jiha.

Kwamishiniyar ma’aikatar Kimiya da fasaha ta jiha Dakta Kulu Abubakar ce ta bayar da kyautar ga gwamna a fadar gwamnatin jiha, a ƙoƙarinta na farfaɗo da haujin don Sokoto ta tserewa tsaranta a Nijeriya.

Gwamna ya nuna farincikinsa ga wannan nasara da aka samu ganin yanda gwamnatinsa ta mayar da hankali ga cigaban ilmi a jihar.

Gwamna Tabuwal ya ce duk wanda zai auna nasarar gwamnatinsa to ya aunata da harkar ilmi, nasarar haujin shi ne nasarar gwamnatinsa gaba ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *