Spread the love

Majalisar dattijai ta kasa ta fara wani yunkuri na gyaran wasu shashe a dokar kasa da aka yi wa gyaran fuska a shekarar 1999, biyo bayan kiran da masu ruwa da tsaki da gwamnatin tarayya ta yi kan batun asusun hadin guiwa tsakanin jihohi da kananan hukumomi, gyaran zai baiwa kananan hukumomi ‘yancin cin gashin kai.

Kundin daftarin gyaran dokar ya tsalke karatu na daya, Sanata Rose Oko daga Cross River shi ne ya gabatar da kudirin.

Majalisar tarayya ta takwas sun yi yunkurin gyaran ba su samu nasara ba. Matukar ana son gyaran ya tabbata sai an samu kashi biyu cikin uku na sanatocin sun amince waton cikin su 109 a samu 73. A majalisar wakillai ma cikin su 360 a samu 240.

A majalisun jihohi ma haka sai an samu rinjayen jihohin da suka aminta da gyaran a jihohin Nijeriya 36 dole 24 su aminta da gyaran dokar kafin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu gyaran ya zama doka.

Dokar za ta yi wuyar samuwa ganin yanda gwamnoni suke wuka da nama a jihohinsu kuma su ne masu nada ‘yan majalisar tarayyar Nijeriya da ‘yan majalisar dokoki na jihohinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *