Gwamnan Sokoto Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya ƙaddamar da rabon tallafin kuɗi naira N20,000 ga mutum dubu 1000, maza da mata ƙarƙashin shirin bayar da tallafin ƙaramar sana’a MICRO BUSINESSES INCENTIVE FUND (MBIF). Gwamnatin Tambuwal ta ƙirƙiri shirin ne don rage raɗaɗin talauci da samar da sana’a ga ‘yan jiha, kuma an ƙaddamar da shi a garin Balle ƙaramar hukumar Gudu.

Gwamnatin jihar ta ware biliyan huɗu (N4 Billion) ga shirin in da mutum dubu 200 ne za su amfana da shirin a dukkan ƙananan hukumomi 23 dake jihar Sokoto.

Kowace ƙaramar hukuma mutum 1000 za su amfana kamar yadda aka fara da ƙaramar hukumar Gudu a zaton Managarciya.

Tambayar da mutanen Sokoto ke yi mine ne dalilin Tambuwal na fara rabon kuɗin a yanzu ba tare da wata sanarwar gudanar da aikin ba, ma’ana majalisar zartarwa ta jiha ba ta zauna ta tattauna lamarin da har za a fitar da bayani ga al’umma don Sakkwatawa su san in da za a ƙone kuɗinsu.

Tambuwal yana faɗi a koyaushe ba a yin gwamnati a ɓoye wanda haka ne a zahiri, amma bai kamata gwamnatin Tambuwal ta riƙa wasa da zaman majalisar zartarwa ta jiha ba, akwai buƙatar a riƙa sanar da jama’a tafiyar da gwamnati lokaci-lokaci.

Rabon tallafin zai rage raɗaɗin talauci a karkara da ƙauyukkan jihar Sokoto in kuɗin sun kai ga waɗanda yakamata ba tare da yanke yawan kuɗin ba.

Bayar da tallafin wasu na danganta shi da nasarar da tallafin da gidauniyar Ɗangote ta samu ne, a yayin da wasu ke ganin siyasar da ke tafe ne Tambuwal ya fara wa shiri, ko mine ne dai lokaci ne alƙalin hasashen mutane.

2 thought on “Rabon tallafin dubu 20 da Tambuwal ke yi a ƙananan hukumomi mine ne manufarsa?”
  1. Koda yake wannan Jaridat ta yan jamiyar APC mai adawa a jihar Sokoto ce, yana da kyaw ta daina siyasantar da labarunta idan tana son mutane suci gaba da karatunta. Managarciya ta cika siyasantar da labarunta. Miye laifin Gwamna idan ya raba tallafi ga masu karamin karfi? Abinda ya kamata Managarciya ta maida hankali akai shine, ta bincika domin tabbatarda wanann aikin alkhairi ya isa ga wadanda akayi domin su, ba siyasantar da wanan labari ba kawai don cimma wani buri na siyasa.

    1. Mu ba ‘yan wata jam’iya muke ba kuma ba jam’iyar siyasa da mu ke yi wa aiki, labaran da mu ke iya gaskiyar fahimtarmu kenan bisa bin ka’idojin aikin jarida. Ku makaranta ku rika adalci in har an kawo labarin da ba ku ji dadinsa ba ku sani don kuna da bangare ne ya sanya haka, kar ku sa Managarciya cikin siyasarku. Mun gode da fahimta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *