Spread the love

Juyin mulkin da Sojoji ke yi ya koma wurin ‘yan siyasa

Tsohon Shugaban kasar Nijeriya Goodluck Ebele Jonathan ya ga laifin ‘yan siyasar Afrika ta yanda cikin hikima suka canja juyin mulkin da soja ke yi  zuwa cikin jam’iyyun siyasa.

Ya yi wadan nan bayanai ne a Okada jami’ar Igbinedion ta jihar Edo bayan an karrama shi da digirin girmamawa a wurin bukin yaye daliban jami’ar  karo na 17.

Ya ce a nahiyar Afrika tsoffin shugabannin kasa sun mayar da juyin mulkin soja a siyasa wanda hakan ba zai cigaba ba.

Ya yi kira ga ‘yan siyasa su daina kashin mutane suna lalata wurarensu, don kawai mutane na son su ma su mallaki na su ofis.

Ya ce abin da ya  faru a jihar Kogi da Bayalsa kwanan nan abin takaici ne a samu mace cikin gidanta a kone, wannan abin ba za ka ga yana faruwa a wuraren da suka san kansu ba. Bai kamata hakan na faruwa a cikin harkokin siyasa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *