Spread the love

Sarkin Musulmi ya ja hankalin al’umma game da cin hanci da rashawa, duk ƙasar da rashawa ta yi mata katutu ba ta samun cigaban da ake buƙata, Sannan ya buƙaci al’umma su zauna Lafiya da fahimtar juna a tsakanin mabiya addinai.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya yi Wannan kiran ne a wani taro da majalisar ƙoli ta ƙungiyar lamurran addinin musulunci ta shirya a Abuja.

Alhaji Sa’ad Abubakar ya yi bayanin Matsaloli da suka Shafi Musulunci da Kuma hanyoyin da Za su Kawo ƙarshen Matsaloli.

Haka kuma ya bayyana musulunchi addini ne na Zaman lafiya, duk da ana Samun Wasu sun dage akan Sai sun aibata shi.

“Kamar kowace ƙasa, a Duniya, Nijeriya tana fuskantar manyan ƙalubale (waɗanda ba dole sai mun zayyano su ba), mun yi imani babu wata matsala a Duniya da babu mafitarta, Idan muka yi ƙoƙarin gyara, Allah ya Sanya Mana Hannu Shikenan, Akan haka ne muka zo domin Samun Mafita game da wayannan matsalolin”. Inji Sa’ad Abubakar.

Jami’i mai kula da harkokin sadarwar zamani ga sarkin musulmi Jamilu Sani Rarah ne ya fitar da bayanan ga manema labarai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *