Spread the love

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta gabatar da mutum 39 bata gari ciki har da mai gari(hakimi) a karamar hukumar Chukun jihar Kaduna.

Hakimin ana  zarginsa da hada baki da masu garkuwa da mutane yana cikin wadanda aka gabatar, jami’in hulda da jama’a na rundunar Yakubu Sabo ne ya jagoranci lamarin.

Daga cikin batagarin akwai gungun masu garkuwa da suka kashe wasu mutane biyu bayan sun karbi kudin fansarsu miliyan 2.8, kuma su ne suka yi garkuwa da daibai mata shidda da malamansu biyu a makarantar  Engravers a Kaduna.

Jami’in ya ce hakimin Unguwar Luka Sama’ila yana yi wa masu garkuwa aiki ta hanyar ba su bayani in sun kammala garkuwa su bashi na shi kaso.

Sama’ila ya karyata zargin yana tare da masu garkuwar amma ya yarda da ya karbi kudin fansa gare su sau uku na farkon sun bashi dubu 100 na biyu dubu 50 na uku ba su bashi komai ba.

Shi bai san komai ba kan suna kisan mutane .   

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *