Spread the love

Daga Sa’adatu Baba Ahmad.

A ƙoƙarinsa na ganin an bunƙasa ilimin addinin musulunci mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi na II ya kai ziyara Jami’ar Alkasimia da ke garin Sharja a haɗaɗɗiyar daular larabawa (United Arab Emirate)

In da ya tattauna da mahukuntan jami’ar domin ganin an samar da gurbin karatu ga mahaddata aAlƙur’ani mai girma, wanda hakan zai ba su damar faɗaɗa iliminsu.
Ana sa ran wannan jami’a nan ba da jimawa ba za ta samarwa matasanmu masu karatun alkur’ani damar gurbin karatu a wannan jami’a mai koyar da harshen larabci tsantsa.

“Muna da makarantu da mahaddata Alƙur’ani a Najeriya musamman a jihar Kano waɗanda za su iya bayar da gagarumar gudummowa a ɓangaren Alƙur’ani da harshen larabci idan suka samu gurbin karatu a wannan jami’a ta Alkasimia.” in ji Sarki Sanusi II

Idan za’a iya tunawa dai Sarkin Kano Muhammad Sanusi II a baya ya samar da bankin musulunci na Jaiz a yanzu ma yana kokarin samar da wata hanya ta samarwa makaranta alkur’ani da masu koyon harshen larabci gurbin karo karatu don inganta iliminsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *