Spread the love

Uwargidan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Hajiya Aisha Buhari  ta yi kira ga shugabannin musulmai a Nijeriya da su yi aiki da abin da suka fadi.

Hajiya Aisha ta yi kiran ne a wajen taron bukin babbar majalisar koli ta harkokin addinin musulunci ga dukkan kungiyoyin musulmai a Nijeriya, ta ce matsayar da aka cimma a taron a sanya ta cikin aiki adomin musulman kasar nan su rika aiwatarwa   a zahiri.

Ta yi kira ga musulmai su amince da matsayar da majalisar za ta dauka musamman ga abubuwan da suka shafi daurewar zaman lafiya da fahimtar juna a kasar nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *