Spread the love

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya ce mutanen Nijeriya sun yi mamakin dokar kisa ga masu kalaman batanci da majalisar dattijai ke kokarin aiwatarwa.

Ya ce wannan dokar matsala ce ga dimukuradiyya, akwai bukatar gyaran fuska ga lamarin da zai kawo cigaba.

Tambuwal ya yi kalaman ne a wurin taron kungiyar Editoci na kasa karo na 15.

Ya ce bai kamata dimukuraɗiya ta zama kamar mulkin soja a wurin kama karya ba. Duk dokar da za a yi kamata ya yi ta zama ta haɗin kai ga ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *