Spread the love

Rundunar ‘yan sandan jihar Edo sun kama wata matar aure kan zargin ta kashe mijinta ta hanyar murɗe al’urarsa har ya mutu.

Mai laifin wadda ake kira Eki Ekhator ta yarda da laifinta da ta aikata a ƙauyen Ukhiri dake ƙaramar hukumar Ikpoba-Okha a jihar Edo.

An gano koyaushe macen tana samun matsala da mijinta a duk san da ya dawo gida ba kan lokaci ba ta yi ta gargaɗinsa bai bari ba.

Wata majiyar ta ce a ranar da lamarin ya faru margayin ya mari matar ne ita ko ta yi wurin wandonsa ta rike al’urarsa ta mirɗe cikin fushi.

Anan take ya faɗi a some bayan an kai shi asibiti aka tabbatar ya mutu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *