Spread the love

Hukumar ‘yan sanda ta jihar Lagos ta gurfanar da wani ɗan shekara 40 Oluwatobi Ajibade kan zargin ya bugi matarsa.

Ajibade yana zaune kan titin Fakeye a unguwar Akute jihar Lagos, yana fuskantar tuhuma biyu na cin zarafi.

Wanda ake zargin bai yarda da tuhumar da ake yi masa a gaban kotun majistare ta Ikeja.

Mai sanya ƙarar ASP Benson ya sanar da kotu wanda ake tuhumar ya aikata laifin a Oke-Aro unguwa a jihar Lagos.

Ya ce wanda ake zargin ya bugi matarsa ne kan bai ga yaransa ba ɗan shekara uku da mai wata bakwai.

Ya ce bugin matar aure ya saɓawa doka sashe 245 a tsarin manyan dokokin laifi na jihar Lagos a 2015.

Manema labarai sun fahimci laifin yana da hukuncin shekara biyu ga wanda ya aikata.

Alƙalin majistare Olufunke Sule ta byar da belin wanda ake zargi dubu 20 da mutum ɗaya wanda zai tsaya mai.

Ta shawarci mai laifin ya kula da matarsa da ɗiyansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *