Spread the love

Majalisar Dokokin Jihar Zamfara Ta Soke Biyan Fansho da alawus na naira Milyan 10 a duk wata ga tsoffin Gwamnonin Jihar

Majalisar dokokin jahar Zamfara ta haramta biyan tsoffin gwamnoni kuɗin fansho, inda tsohon gwamna ke tashi da naira miliyan 10 a duk wata.

Tshon gwamna Abdul’aziz Abubakar Yari ne ya tayar da maganar in da ya rubutawa gwamna mai ci ya biya shi kuɗinsa tun da haƙƙinsa ne.

Bayan haka ne gwamna Bello Muhammad Matawalle bai biya kuɗin ba, sai ya turawa majalisar dokoki neman yi wa dokar da aka samar lokacin tsohon gwamna gyaran fuska, an samu nasara an kammala gyaran dokar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *