Spread the love

Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyar PDP ga zaɓen 2019 Atiku Abubakar ya dawo Nijeriya bayan share kusan wata bakwai a Dubai haɗaɗɗiyar daular larabawa.

Mai baiwa Atiku shawara kan harkokin yaɗa labarai Paul Ibe ya tabbatarwa manema labarai dawowar.

Atiku ya ziyarci mahaifarsa ya yi gaisuwar ɗaya daga cikin mataimakansa da ya rasu kwanan nan.

Ya yi bukin murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

Atiku ya cika shekara 73 a duniya abin da wasu ke ganin yanzu ne yafi dacewa ya riƙa ƙasar don sauya mata alƙibla da cigaba fiye da yanda ake yanzu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *