Spread the love

Muƙaddashin shugaban tuntuɓa na Arewa Alhaji Musa Liman Kwande ya ce mutanen Arewa za su zaɓi ɗan yankin ne ba tare da la’akari da kowace jam’iya yake.

Ya ce ya bayyana ra’ayinsa na goyon bayn ɗan arewa ne a matsayinsa ɗan Nijeriya ba ra’ayin ƙungiyar tuntuɓa ta Arewa ne ba.

Ɗan Arewa da aka san yana da nagarta ya tsaya takara da wani daga kowane ɓangaren ƙasa mutane su zaɓi wanda suke so a yi dimukuraɗiyya.

Nijeriya ƙasar mu ce dole mu haɗa kai mu kawo cigaba duk da bambancin yankin ana ciyar da Nijeriya gaba.

Alhaji Kwande ya yi kira ga ‘yan siyasa su riƙa karɓar sakamakon zaɓe, su daina sanya matasa bangar siyasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *