Spread the love

Matar aure mai ƙarancin shekaru mai suna Ruƙayyat Abdulrahmon an zarge ta da kashe ɗanta mai shekarru uku da haifuwa a garin Osogbo a jihar Osun.

Matar ta yarda ita ce ta jefa ɗansu guda da suke da shi mai suna Ganiyu cikin rijiyar dake cikin gidansu a unguear Kola Balagun a Lahadin da ta gabata.

Ta ce ta kashe yaron ne domin ta hukinta mijinta Raheem da ya tafi kotu yana neman a raba aurensu.

Matar ta ce ba ta jin daɗin auren babu zaman lafiya a zamantakewarsu.

Kotun Shari’ar musulunci ta shiga lamarin ta baiwa ma’auratan wata uku su sulhunta kansu kafin daga baya mijin ya nemi a raba shi da matarsa.

Matar ta kashe yaron kwana biyar suka rage cikin kwana 90 da kotu ta ba su in ba a samu silhu ba a rabu.

Kukan ma’auratan ya tayar da mutanen unguwarsu da safe a lokacin da suka fito neman margayin, wanda suka ce tare da shi suka kwana a ɗaki ɗaya. Mutanen unguwa sun taya su neman ɗansu a gidaje daban-daban ba a ganshi ba.

A lokacin da wata Budurwa ta je ɗibar ruwa a rijiyar ne domin ta yi wankin kayanta na sawa ta ga gawar yaron saman ruwan.

‘Yan sanda sun kama mahaifan yaron a matsayin waɗan da ake zargi da wasu maƙwabtansu dake cikin gidan.

Bayan haka ne mahaifiyar yaron ta ƙarɓi laifinta ta ce ita ta kashe shi domin ta hukunta mijinta tana son kar ya amfana da zamantakewar da suka yi.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Osun Mustafa Ketayeyanjue ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce matar ta baiwa ‘yan sanda haɗinkai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *