Spread the love

‘Yar wasan Turanci Nnenna Orji a zantawarsa da manema labarai ta bayyana abin da take so ga namijin da za ta zama da shi.

“Abin da nake so ga namiji ya zama mai tsoron Allah, ina son mutum wanda zai fahimce ni mu haɗa kai mu yi tafiya tare, bana son wanda zai hanani kasuwancina, bana son mai kuɗi, sai dai wanda yake da wadata da zai iya kula da ni da yaranmu da za mu haifa, haka bana son wanda nafi arziki.” a cewar Nnenna.

Ta amsa tambayar ko kafin ta taka rawa a fim sai an yi amfani da ita. Ta ce in mutum ya yi haka mi ya samu hakan baya da amfani ka ba da abu don a ba ka wani abu, yakamata kasan abin da kake yi.

Ta ce ita ba za ta yi abin da abokiyarta ta yi ba na auren tsoho amma ba ta ga laifinta ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *