Spread the love

Muhammad Tijjani Maibrah.

A kokarin gwamnan jihar Yobe, Gwamna Mai Mala Buni na farfado da al’ummar yankin da rikicin Boko Haram ya ɓarnata sosai, gwamnan ya ziyarci manyan aiyuka guda biyu dake hedikwatar ƙaramar hukumar Gujba, Buni-Gari.

Gwamna Mai Mala Buni, ya fara da ziyartar babban asibitin Buni-Gari, inda Gwamnatin shi ta bada aikin sabunta asibitin a wata biyu da ya wuce, inda gwamnan ya ganewa idon shi yadda aikin yake wakana.

Daga bisani Gwamna Buni, ya wuce cikin garin Buni-Gari domin ganewa idon shi aikin shimfida Hanyoyi da gwamnatin shi take yi, a jawaben shi, ya yaba kokarin ‘yan kwangilar bisa kokarin na yin aiki akan kokaci, ya yi kira da su kammala aikin akan Lokaci kamar yadda akayi Yarjejeniya basu Kwangilar aikin.

Gwamna Buni, ya jinjinawa jami’an tsaro bisa kokarin da suka yi na samar da tsaron rayuka da dukiyar al’ummar yankin, daga bisani yayi kira da su bude kasuwar Garin Saboda al’umma su fara kasuwanci da hada-hadar Kasuwanci a yankin domin inganta tattalin arziki, saboda al’ummar yankin su koma muhallinsu.

A jawaben Gwamna Mai Mala Buni, ya bayyana cewa, aikin gina Hanyoyin cikin gari, zai fara ginawa a ƙananan hukumomi 3 Damagum, Babban Gida da Jajimaji hedikwatan ƙananan hukumomin, Tarmuwa, Karasuwa da Fune.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *