Spread the love

Da yawan mutane sun rasa ransu a ɓangaren mahara da mutanen gari a jihar Adamawa a wurin kare kan su ga harin maharan.

Ƙauyen da aka kawowa hari Shuwa-kala’a a ƙaramar hukumar Hong a jihar Adamawa, wanda ya yi magana da manema labarai kan harin ya ce ba zai iya ba da yawan mutanen da suka rasa ransu ba, a dukan ɓangarorin sun rasa ran mutanensu.

Ya ce da safe ne maharan suka zo har suka tare wani manomi da zai je gona bayan ya dawo ne ya danar da jama’ar gari abin da ya garu gare shi, daga nan ne ‘yan sakai na garin suka haɗu domin kare kansu anan suka tinkari maharan an samu rasa rai da yawa.

Rundunar ‘yan sandan Adamawa ba su bayyana yawan mutanen da suka rasa ransu a harin ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *