Ina son in tafi makaranta kafin in yi aure—Aisha Tsamiya

Sanannar ‘yar wasan Hausa Aisha Aliyu wadda aka fi sani da Aisha Tsamiya ta bayyana ƙudirinta na son sai ta koma makaranta kafin ta yi aure.

“ina son in samu ilmi in kammala karatuna kafin kafin in yi aure, duk da nasan ƙaddara na iya canja burina ko yaya dai ina son in yi abin da yake daidai, Allah ne mai zatar da lamari mu ƙudiri ne namu.” in ji Tsamiya ‘yar wasan Kannywood.

Ta ce ta ƙara samun ɗaukaka ne a lokacin da ta yi fim ɗin ɗakin Amarya da So ba ta yi tsammanin ta samu shahara lokaci ɗaya ba da har zai kai ba ta iya tafiya unguwa ko kasuwa ba tare da mutane sun gane ta ba suna kiranta.

Tsamiya ta ce ta samu nasara a rawar da take takawa a finafinnai, burinta a yanzu ta fara bayar da umarni a fim kamar yadda Muhibbat Abdussalam, wannan ƙudirinta ne na biyu bayan karatu yanzu haka tana karatu a jami’ar Arewa ta Yamma wadda gwamnatin jihar Kano ta gina.

Aisha Tsamiya ta kwashe fiye da shekara shidda a masana’antar shirya finafinnai na Hausa, tana cikin mata masu taimakawa jama’a duk da ita ba ta cikin masu kuɗi mata a harkar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *