Spread the love

Babban sakatare a ma’aikatar lafiya ta jihar Yobe Hamidu M. Alhaji ya ce jihar su na cikin jihohin ƙasar nan da ciwon gyada ya yi yawa.

Ya ce suna da kes na cutar kusan dubu 3225 yaro 34 suka rasu sanadiyar ciwon tun daga watan Junairu zuwa Okotoban wannan shekara.

Babban sakataren ya bayyana haka a lokacin ƙaddamar da bayar da rigakafin cutar ciwon gyadar a fadar uban ƙasar Bulabulin a Damaturu.

Ya ce gyada na cikin ciwo mai kashe yara ko ya illata su nan take musamman a in da al’umma suke da yawa.

Ya ce gyada na lahanta yaron da ba a yi wa rigakafin ba lokacin da yake wata biyar har shekara 15.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *