Spread the love

Hukumar da ke kula da bashi ta ƙasa(DMO) ta ce bashin da ake biyar Nijeriya a yanzu ya kai Tiriliyan 25.7.

Babban Darakta na hukumar Ms Patience Oniha ya sanar da hakan a lokacin da yake yi wa kwamitin majalisar waƙillan Nijeriya kan kadarorin gwamnati.

Ya ce a watan Yunin 2019 bashin da ake biyar Nijeriya ya kai Tiriliyan 25.7 wanda gwamnatin tarayya da jihohi da birnin tarayya Abuja suka ci.

Ya ce sun haɗa wannan bashin gaba ɗaya gwamnatin tarayya ta ci kashi 80 na bashin.

Kuma a bashin sun gano kashi 32 ne aka ciwo a ƙasashen waje kashi 68 na cikin gida ne.

Ya ce hukumarsu ta gwamnati ce da aka ƙirƙira a 2000 ganin yanda bashi ya yi wa ƙsar ka tutu a lokacin domin hukumar ta shiga gaba a samu sauƙi ga lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *