Spread the love

Bayan da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukuncinta na tabbatar wa Gwamna Aminu Waziri Tambuwal kujerarsa ta gwsmna a jawabinsa na godiyar Allah da mutanen Sokoto ya yi kira ga abokan hamayya su zo su yi tafiya tare don gina jihar Sokoto.

Ya yi alƙawalin tafiya tare da ‘yan adawar a cikin gwamnatinsa su zo a haɗa kai a yi tafiya tare.

Tambuwal ya tunatar da ‘yan adawa mulki na Allah ne yana baiwa wanda ya ga dama don haka su zo a haɗa kai a ciyar da jiha gaba don ba su da wata jiha sai Sokoto jihar su ce baki ɗaya.

Ya nemi al’ummar jiha su ci gaba da ba da haɗin kai a ciyar da jihar gaba ya saɗaukar da nasararsa ga Allah.

Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko a jawabinsa da al’ummar da suka taru gidansa bayan sallar jumu’a ya ce ‘zamanmu na musulmi komi ya zo gare mu daga Allah ne mu godewa Allah ya yi mana komai’

“in da rai da rabo tafiya da magana ba su ƙare ba cikin yardar Allah, shari’a har yanzu ba ta ƙare ba yanzu ne an ka fara cikin yardar Allah.”a cewar Wamakko.

Ya ƙara da faɗin “tafiyarmu ba faɗa da zage-zage da buge-buge, ba da kowa muke faɗa ko jayayya ba muna neman ƙwato zaluncin da aka yi mana, za mu yi ƙoƙarin ƙwato haƙƙinmu, mu bar komi in ya zo daga Allah ne.” in ji Sanata Wamakko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *