Spread the love

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ce shi ba zai nemi wa’adin mulki a karo na uku ba.

Ya yi rantsuwa da Alƙur’ani ba zai nemi ƙarin wa’adi bayan ya kammala nasa ba zai yarda da shirin ba kowa ya tsara shi zai janye wasu su zo su ma.

Ya ce tarihi ba zai yafewa waɗanda suka bari jam’iyar APC ta mutu bayan mulkinsa ba don haka akwai buƙatar tashi tsaye a yi aiki tuƙuru jam’iyar ta ci gaba da jan ragamarta a ƙasa.

Shugaba Buhari ya yi waɗan nan kalamai ne s wurin taron shugabannin jam’iyarsa na ƙasa ya ce duk wanda y raba jam’iya saboda biyan buƙatar ya sani ba za a tuna da shi ba a matsayin jagora.

Ya nuna gamsuwarsa kan haɗin kan da ake samu a jam’iya da yanda aka samu fhimta tsakanin majalisar zartarwa da ta dokoki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *