Spread the love


 APC za ta ɗaukaka ƙara a kotun ƙoli kan nasarar da Tambuwal  ya samu.

Daga Sadiya Jabo

Jam’iyar APC a jihar Sokoto za ta ɗaukaka ƙara a kotun ƙoli  kan nasarar da gwamnan jihar Sokoto Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya samu a kotun ɗaukaka ƙara mai mazauni a Sokoto in da ta tabbatar da hukuncin da kotun sauraren ƙara ta yi amatsayin daidai.

 A jawabin mai baiwa APC shawara kan harkokin shari’a, Barrister Bashir Mu’azu Jodi ya ce suna da hujjoji masu ƙarfi da za su ɗaukaka ƙara zuwa kotun ƙoli don ba su gamsu da hukuncin ba.

Ya ce neman haƙƙi a gaban shari’a yanzu aka fara ba wani damuwa kan wannan hukunci tun da za a tafi gaba. Da yardar Allah za su samu nasara a shari’a ta gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *