Spread the love

Babbar kotu a jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin mai Shari’a Usman Na’Abba ta soke karin masarautun da gwamnatin jihar Kano ta kirkiro wadda Gwamnan Abdullahi Umar ya samar ya ba su sandan kama aiki.

A ranar 8 ga watan Mayu, Gwamna Abdullahi Ganduje, ya mikawa majalisar jihar bukatar karin masarautu huɗu tare da manyan sarakuna a garuruwan Bichi, Rano, Karaye da Gaya na jihar Kano, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

A yayin yanke hukunci a ranar Alhamis, kotun ta ce, majalisar jihar Kano ta yi karantsaye ga tanadin sashi na 101 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, wanda ya ba ‘yan majalisar damar zartar da doka.

Tun bayan fitowar maganar kirkirar sabbin masarautu a jihar Kano, Mutane da yawa sun ta tunanin Gwamna Ganduje na yakar Sarki Sanusi ne ta ruwan sanyi bayan banbancin da suka samu a zaben 2019.

A gabanin zaben kujerar gwamnan jihar Kano, wata majiya da ke da kusanci da gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da cewa, gwamnan na sane da ganawar da Sarkin yayi da Kwankwaso da Abba gida-gida, dan takarar kujerar gwamnan jihar karkashin jam’iyyar PDP.

Wata majiyar ta ce, Basaraken ya umarci hakimai da su goya wa Abba gida-gida baya yayin zaben da za a yi tare da tabbatar da cewa APC ta yi warwas a zaben.

Dukkan wadannan abubuwan da Sarkin ya yi, ba boyayyu bane a wajen gwamnan. Don haka ne ya bi cikin ruwan sanyi ya ke ramuwar gayya. Cikin ramuwar gayyan ne kuwa ya kirkiro masarautu da sarakuna 4 masu karfin iko iri daya da Sarki Sanusi II.

Al’umnar garin Ƙaraye sun fito zanga-zangar nuna rashin gamsuwa da hukincin jim kaɗan bayan zartar hukuncin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *