Spread the love

Gwamnan jihar Sokoto Aminu waziri Tambuwal ya ƙaddamar da sabuwar ƙungiyar ƙwallon ƙafa da za ta riƙa Waƙiltar jihar a wurin wasan tamola. Tambuwal ya nemi ƙungiyar su yi ƙoƙari sosai su dawo da martabar jihar a fannin wasan ƙwallon ƙafa.

Gwamnan ya tabbatar wa masoya ƙwallon ƙafa gwamnatinsa za ta samar da yanayi mai kyau ga masu wasanni maza da mata don su nuna bajintarsu.

Ya nuna gamsuwarsa ga sabuwar ƙungiyar domin yanzu za ta iya gogaiya da kowace ƙungiyar wasa a ƙadar nan a rukunin zakarun ƙwallo na ƙasa.

Tambuwal ya ƙarfafi ‘yan wasan da za su fara gasar cin kofin zakaru na Nijeriya da ƙungiyar ƙwallo ta Neja tonados dake garin Minna a ranar Jumu’a mai zuwa, su samu nasara su dawo da gida bayan sun gama lallasa abokiyar karawarsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *