Spread the love

Ɗan ƙwallon Nijeriya, Ahmed Musa Ya ɗauki nauyin Karatun Matasa 100 a Jami’ar SkyLine dake Kano domin ƙara bunƙasa ilmin mutanen jihar da yankin Arewa gaba ɗaya.

Shahararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Nijeriya, Ahmed Musa, ya ɗauki nauyin biyan kudin makarantar matasan 100 a sabuwar jami’ar SkyLine.

Jami’ar ce ta bayyana hakan a yau Laraba, inda dan wasan kwallon kafa wanda ya fi duk wani dan wasan kwallon kafan Nijeriya kada kwallo a raga, zai kasance fuskar jami’ar sannan kuma zai taimakawa jami’ar wajen habbaka harkokin wasanni.

Abin da wannan matashin ya yi abin a yaba ne da yankin arewa za su riƙa samun irin shi mai son taimakawa ga haujin cigaban matasa da an samu abin da ake so ga bunƙasar ilmin mutanen arewa.

Hakan nuna kishi ne da son taimakon matasa su tashi daga in da suke a yau zuwa mataki na gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *