Spread the love

Tsohon shugaban kasa Dakta Goodluck Ebele Jonathan zai iya fuskantar dakatarwa daga jam’iyarsa ta PDP saboda zargin da ake yi masa na yi wa jam’iyar zagon kasa ya hada kansa da APC abin da ya yi sanadiyar kayar da PDP a jihar Bayalsa a zaben da ya gabata.

Wasu jigogin jam’iyar ma sun sha kaye a jihar bayan shekara 20 suna mulki, wasu jigogin jam’iyar na ganin  yakamata a bincike lamarin faduwa zaben.

Wata majiya kwakkwara ta ce jam’iyar PDP ta kammala shirin yin taro domin ta duba yanda ta sha kaye a zaben Kogi da Bayalsa.

Abin da wasu ke ganin kamar taron za’a yi shi ne domin dakatar da Jonathan ga abin da ya aikata har PDP ta sha kasa a zaben.

Managarciya na ganin dakatar da Jonathan yana iya haifar da matsala ga jam’iyar PDP a kudancin Nijeriya ganin yanda yake da dimbin magoya baya da zamansa jigo a siyasar yankin da Nijeriya gaba daya.

PDP yakamata su dubi dalilin aikata abin da ya yi kafin su dubi abin da ya yi domin yi masa adalci, ka da jam’iyar ta fada wani sabon rikici da zai iya karya jam’iyar da zai cigaba da yi mata lahani a zabuka na gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *