Spread the love

Mahara sun kai farmaki a kauyen karaye yanki karamar hukumar Gummi  jihar Zamfara sun kashe mutum 14.

Mazauna kauyen sun ce maharan sun zo da yawa saman babura da karfe 9 na dare suka rika harbin mutane suna cinnawa gidaje da shaguna da ruhewa da wasu abubuwa na garin wuta.

Wani dan  yankin a zantawarsa da manema labarai ya ce da farko maharan sai da suka tsaya kauye Kurfa suka karbe baburan mutane da satar kayan shagunan mutane, kafin su zo kauyensu.

Hankalin mutane ya tashi a lokacin da aka rika ganin maharan suna gittawa a dajin garuruwan.

Tun bayan da aka yi sulhu da maharan a watan Yunin wannan shekara kai harin ya yi sauki sai ga shi yanzu kuma abin na son komawa danye.

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Zamfara ta tabbatar da faruwar lamarin na kawo sabon hari .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *