Daga Munzali Gaya Waraka.

A Shekarar 2019 Jam’iyyar APC ta yi Babban kuskure Wajen fitar da ‘yan takarkaru Wajen Zaɓen cikin gida Wanda Wannan Shi ne ya haifar mata da tsiya-tsiya ta ci Zaɓe irin wannan Matsalolin ne har yanzu basu warware ba.

Matsalolin suka zamar mata silar asara rasa Wasu kujeru a Kotu, ana tsammanin Wasu na iya rasa kujerunsu domin har yanzu da akwai kujerun da ba a gama Shari’ar su ba.

To Haka yanzu ana ganin abin sake Faruwa a 2024 Domin Tun Daga yanzu akwai Yan Takarkaru Wanda ba za su iya Cin akwaitin kofar Gidansu bama.

Kuma Sun yo ca Suna So Gwamnan jihar kano Ya Sahale musu Su Tsaya Takarar Gwamnan jihar kano.

To Mutukar aka bi Son Zuciya da kwadayin abin Duniya kamar yadda aka yi a 2019 To lallai APC a jihar kano Za ta yi wanwar matsawar Bata tsayar Da ‘Yan Takarkaru masu kwaliti da nagarta.

Kuma wallahi idan APC ta Faɗi a jihar kano to Kuwa ita Da mulki a jihar kano Sai dai a Zance idan ya Tashi ko in ce a Tarihin Siyasar jihar kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *