Spread the love

BINCIKE
Matar Bahaushe ta fi Kowace Mace Gata A Duniya Amma Ita Ce Ta Fi Gasa Wa Namiji Aya A Hannu
A iya binciken da na yi matar Malam Bahaushe tana da gata sosai sama da sauran matan kabilunmu, domin Malam Bahaushe bai yarda ya ga matarsa ta fita tana aikin karfi ko wahala ba.
Shi duk talaucin sa ya fi so matar sa ta zauna a gida shi ya fita ya yi aikin karfin ko wahalar domin ya nemo musu abin da za su ci shi da ita da yaransu.
Da wuya ka ga matar Malam Bahaushe tana zuwa daukan ruwan da zasu sha ko nemo abin da zasu ci, ko daukar nauyin karatunta ko daukar nauyin gidanta da na yaranta ko da kuwa mai hali ce.
Malam Bahaushe idan mai hali ne ma hatta girki da wanki ko wanke-wanke ya haramtawa matarsa sai dai ya dauko masu yi mata hidima… Ita sai dai ta kwanta ta ci ta sha tayi ibada sai kuma kula da tarbiyyar yaransu kawai… Ko Unguwa za ta akwai direba idan ba mota a ba ta kudin a dai daita sahu.
Amma wallahi abin takaici da haushi sai kaji Malam Bahaushe kullum yana kuka da matarsa… Sam ba ta bashi haɗin kai kullum cikin tashin hankali da ɗaga masa hankali take…

Da yawa daga cikin ire iren waɗannan matsalolin ne kan sa wani namiji ƙarin aure ko Allah zai sa ya dace ko kuma yayi tunanin tsallakawa ya auro wata ƙabilar ta daban wacce yake tunanin zai samu zaman lafiya da ita.
Wai kuwa matanmu na ƙasar Hausa suna lura da yadda matan wasu ƙabilun ke fama da aikin ƙarfi domin ɗaukar nauyin mazansu da yaransu?

Ta dalilin aikin ƙarfin da suke yi har jikinsu ya murɗe ya zama irin na maza?
Kuma duk da haka suna girmama mazajensu duk da irin yadda suke gallaza musu kuwa?
Wasu matan ƙabilun su fita kiwon dabbobi ko yin itacen girki, wasu su yi aikin kafinta ko ɗaukar bulo ko gini, wasu da ciki ko goyo suke wannan aikin kuma su samo kudin su dawo gida su girka abinci su ci su da mazajensu da yaransu…

Ke kuma matar Malam Bahaushe me ki ka sani game da irin waɗannan aiyukan wahalar?
Ni dai wallahi na kasa fahimtar me yake damun wasu daga cikin matan Malam Bahaushe ne, ko dai dadi ne yayi musu yawa?

Matan wasu na ƙoƙarin faranta ran mazajensu mazan ne ke hasala su ga irin hidimar da suke yi domin rashin ilminsu na sanin zamantakewar rayuwa.

Al’ada da yanayin wayewar wasu matan ke hana masu yin biyayya da hidimtawa mazajensu, abin da yakamata a samu wasu jama’a da za su riƙa wayar da kan matan su gane yi wa mazansu hidima ba bauta ne ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *