Spread the love

‘Yan bindiga saman Raƙumma sun kashe maharba biyar a ƙauyen Gombi dake jihar Adamawa.

A majiyar da aka samu maharan sun yi wa maharban kwantan ɓauna ne a cikin daji na kusa da Zumo ƙauyen dake tsakiya arewa da gabadcin jiha.

Ɗaya daga cikin maharban da ya nemi a sakaya sunansa ya ce mutanen ‘yan Boko haram ne da ke neman jami’an tsaro da ‘yan ƙungiyar sintiri.

Ya ce ‘yan boko hsram ne suka kashe mana mutane biyar a ƙauyen Zumo cikin Gombi. ‘Yan bindigar sun zo saman rakumma suka farma maharbanmu, bayan nan sun ƙwace shanun mutane.

Jami’in hulɗa da jama’a na ‘yansanda a Adamawa Suleiman Nguruje ya ce mahara ne suka kashe maharban, jami’an tsaro da maharban suna nan suna sintiri su kama mutanen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *