Spread the love

Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar a birnin Ibadan jihar Oyo ya ce dalibai mata musulmi a dukkan fadin Nijeriya suna da damar da kundin tsarin mulki ya ba su na sanya hijabi a makarantun da suke karatu.

Kan haka akwai bukatar uwaye musamman su kare hakkkin ‘ya’yansu ga abin da suke da dama a tsarin doka.

Sarkin a lokacin da yake yi wa al’ummar musulmi bayani a wurin taron babbar majalisar muulmi ta kudu masu yamma wanda aka yi wa take da ‘hadin kan musulmi cikin sabbin matsalolin siyasar Nijeriya’ an gudanar da taron ajami’ar Ibadan.

Sarkin musulmi ya gargaɗi mudulmai su zama masu bin doka da oda kar du yi abin da za a ce masu tir, su bar sukar junnansu domin a zauna lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *