Spread the love

Da yawan mutane in suka zo yin aure shekaru na cikin abubuwan da suke dubi in za su yi aure ko za su aurar.

A gefen mata baka jin suna maganar in za su yi aure sun fi son su samu wanda ya girme su da shekara biyar ko fiye, amma a gefen maza za ka ji suna yin wannan gwajin a maganar aure.

A bin da Mujallar Maganagarciya anan take son tambaya shi ne ‘Yakamata shekarru su shiga cikin tsarin aure’?

Ka fahimta anan ba mu maganar yara kanana da ba su isa yin aure ba muna magana kan manyan mutane da suka kai munzalin yin aure.

M.A Faruk wani magidanci ne a jihar Sakoto ya ce shi yana ganin yakamata shekarru su shiga cikin tsarin ko ba komai aure wani lamari ne da ake domin samun fahimta da taimakon juna in ka auro wadda ta fi ka shekarru yana yiwu ta kasa yi maka biyayya yanda ya kamata.

Zara’u Yusuf mai shekaru 37 ta ce mijina ya bani shekara 15 da haihuwa amma yana kulawa dani yanda yakamata, yana girmamani da kare ni ga duk wadanda da ke son zaluntata, kafin mu yi aure mutane sun yi ta fadin domin mi zan aure wanda ya girman da yawa haka wasu ma cewa suke yi zan aure shi ne saboda kudi, ga shi yanzu aurenmu ya kai shekara takwas da diyanmu muna tare.Bai kamata a rika sanya maganar shekarru a tsarin auratayya ba.

Karima Ya’u ta ce mace da namiji su daina kula maganar shekarru a aure domin yana cikin abin da ke kawo matsalar yin aure a kasar Hausa in dai mutum yana da kirkinsa da harkar yi sana’a ko aikin gwamnati ki aure abinki. Shi ko namiji da zaran ya samu ‘yar gidan mutunci mai addini ya auri abarsa don Allah a share maganar shekarrun nan na al’ada.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *