Spread the love

A jihar Kogi da ke arewa ta tsakiyar Najeriya, ana ci gaba da dakon sakamakon zaben gwamna, wanda rikici ya dabaibaye.

Masu sa-ido kan zabe sun yi zargin cewa an yi magudi a zaben da sayen kuri`a da firgita masu zabe, lamarin na iya shafar sahihancin sakamakon zaben.

A halin da ake ciki dai an kammala tattara sakamakon zaben a matakin gunduma da kananan hukumomi.

Ayanzu hanksli zai koma cibiyar tattara sakamakon zaɓe zabe dake Lokija don ganin yadda za a hada alkaluma, kana a sanar da sakamakon zaben gwamna, wanda aka kammala jiya.

Masu sa-ido a kan zaben da dama
sun bayyana an samu yamutsi a rumfunan zabe a wasu yankuna jihar Kogi, musamman ma yadda ‘yan bangar siyasa suka dinga cin karensu ba babbaka.

Sun dinga harba bindiga domin su tarwatsa jama’a, suna kuma fasa akwatunan zabe, suna kuma sace wasu.

A wata mazabar ma, irin Adankolo da ke gefen birnin Lokoja, mutum uku ne suka rasa rayukansu sakamakon harin da ‘yan bindiga suka kai, wadanda BBC ta tarar ana kokarin yi musu janaza.

Mutum 23 da uku ne suka takara kujerar gwamna a zaben, amma gwamna Yahaya Bello na jam`iyyar APC da Musa Wada na jam’iyyar PDP da kuma Natasha Akpoti ta jam’iyyar SDP su ne a sahun gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *