Spread the love

Daga Comr Abba Sani Pantami.

Jam’iyyar APC na kan kafa tarihi a jihar Bayelsa yayinda take gaba da jam’iyyar hamayya, PDP, da tazarar 86,330 a sakamakon kananan hukumomi shida cikin takwas na jihar.

Yayin da dan takarar APC, David Lyon, ya samu kuri’u 206,260, Duoye Diri na PDP yana da kuri’u 119,330.

Kawo yanzu, hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta sanar da sakamakon kananan hukumomin Yenagoa, Ogbia, Brass, Nembe, Kolokuma/Opokuma da Sagbama.

Sakamakon da ake saurara yanzu sune karamar hukumar Southern Ijaw da Ekeremor.

An tafi hutun rabin lokacin awa daya kafin a cigaba.

Har zuwa haɗa rahotonmu ba a dawo hutun ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *