Spread the love

Wannan al’amari dai ya faru ne a ranar biyar 5 ga watan Mayun shekara ta 2019 da muke ciki, inda wani mutum mai suna Zahraddin Ado ya dauki matar ya kaita gidan wata ma’aikaciyar lafiya mai suna Jummai don ta zubar mata da ciki.

Sai dai a yayin da aka yiwa matar aikin zubar da ciki, a dakin tiyatar da jummai ta bude a gidanta, nan take ta rasa ranta.

An gurfanar da wadanda ake zargin a kotun majistiri mai lamba 30 ƙarƙashin mai shari’a Yusuf Sulaiman. Lauyan gwamnati Barista Lamido Soron dinki ya gabatar da tuhumar, inda ya bayyana cewar ana zargin mutanen da hada baki da aikata kisan kai.

A ƙarshe dai mai hukunci ya sanya ranar Litinin 18 ga watan da muke ciki domin cigaba da sauraron shari’ar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *