Spread the love

Daga Bangis Yakawada.

Hukumar jarrabawar Afirka Ta Yamma (WAEC) ta fitar da sakamakon jarrabawar karshen shekara wato Nuwamba/Disamba WAEC ta bayyana cewa jimlar dalibai 33,304 ne suka yi nasarar lashe darusa biyar ciki har da lissafi da Ingilishi.

Hukumar ta rike sakamakon jarrabawar dalibai 9,457.

Hukumar jarrabawar ta WAEC wacce ta saki sakamakon jarraawar a jiya Juma’a ce ta bayyana hakan.

Hukumar, ta hannun Olu Adenipekun, Shugaban ofishinta na Nijeriya, ta ce ta kuma rike sakamakon jarrabawar dalibai 9,457. An ruwaito cewa Adenipekun, wanda ya yi Magana a Legas, ya ce dalibai 94, 884 ne suka yi zaman zana jarrabawar. Ya ce kaso 35.10% na daliban sun yi nasarar lashe darusa biyar da suka wajaba zuwa sama.

A kamanceceniya, kaso 35. 64% na dalibai ne suka lashe darusa biyar a 2019. Mun rawaito cewa WAEC ta fara sakin sakamakon jarrabawar Mayu/Yuni 2019 a baya inda Adenipekun ya sanar da cewa dalibai 1,596161 ne suka yi rijistan jarrabawar daga sanannun makarantun sakandare 18,639 a Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *