Daga Comr Abba Sani Pantami.

Shugaba Muhammadu Buhari na hanyarsa ta dawowa Najeriya daga birnin Landan, kasar Ingila yanzu haka. Premium Times ta bada rahoto.

Jirgin shugaban kasa ya tashi daga filin jirgin saman Stansted dake Landan ne misalin karfe 3:27 na rana.

Majiya daga fadar shugaban sun bayyana cewa an umurcesu su kasance a filin jirgin saman Abuja daga misalin karfe 7:30 na dare domin tarban shugaban kasan da ake sa ran saukarsa misalin karfe 9 na dare.

Bayan halartan taron karfafa tattalin arziki a Saudiyya, shugaba Muhamadu Buhari ya garzaya kasar Ingila da sunan ziyarar kansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *