Spread the love

Ta amince za ta baiwa mijinta sadakinsa ya sake ta kan zarginsa da yin fyaɗe.

Fatima Ishaƙ matar aure ce a jihar Kaduna ta maka mijinta Hassan Haruna kotun shari’a kan zargin ya yi fyaɗe.

Matar tana zaune da mijinta a cikin garin Kaduna ta hannun lauyanta M.S Abdullahi ta ce ba ta iya cigaba da zama da mijinta Haruna.

Abdullahi ya ce wadda yake tsayawa ba ta iya cigaba da ganin girman mijinta kan haka take son kotu ta raba aurensu kuma a shirye take ta biya sadakin da mijinta ya biya na aurenta a lokacin dubu biyar ya bayar a 2006.

Sannan ta kuma nemi abar mata ɗiyanta huɗu wurinta ubansu ya riƙa bayar da dubu 20 kowane wata na lalurar yaran.

Haruna a kotu ya ƙaryata zargin da ake yi masa.

Ya ce in dai kan zargin fyaɗe ne take son rabuwa da shi, tau shi zai iya rantsuwa da ƙur’ani bai aikata laifin ba. Amma shi zai iya sakinta yanda ta buƙata.

Alƙali Ɗahiru Lawal ya raba auren tare da bayar da umarnin mai ƙarar ta biya sadakin tsohon mijinta Haruna dubu 15 don su za su za su iya zama kwatankwacin waɗanda ya biya a 2006.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *