Spread the love

Neman maye gurbin kujerar jagoran majalisar wakillan Nijeriya wadda dan majalisar wakillai Alhassan Ado Doguwa yake sama kafin kotu ta soke zabensa an fara  neman ta asirce.

An fahimci ‘yan majalisa guda uku da suka nemi kujerar tare da Doguwa a wannan majalisa ta 9 sun fara nema a karkashin kasa tun bayan da kotu ta soke zabensa.

Wani dan majalisar wakillai a jam’iyar APC ya ce majalisa ba za ta bar kujerar ba kowa ba a tsawon lokaci.

Ya ce ba wani hikimar barin kujerar haka nan tun da wanda yake sama ya koma ruwa wajen neman a sake zabensa kotu ta ce a yi zaben cikin wata uku(kwana 90).

Wata majiya ta ce an fara matsa wa Kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila ya cike gurbin. Amma magoya bayan Doguwa suna son a rika jan kafa.

Ana ganin dai bayan majalisa ta amince da kasafin kudin shekara mai kamawa ta 2020 za su je hutu, in ba a samu nasarar maye gurbin Alhassan ba yana iya dawowa saman kujerarsa bayan hutu, in ya ci zabe kenan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *