Spread the love

 

A duk duniya kididdiga ta nuna a yanzu masu fama da ciwon shuga sun kai  kimanin mutane miliyan 366.

Nijeriya ce ke da  kashi biyar na masu cutar(5%)  in da mutum miliyan 10  ke fama da ciwon.

A Nijeriya mutanen jihar Kano sun fi kowa yawan masu cutar(3-4)  A  duk sati ana samun bullar cutar a kasar baki daya mutum 10 zuwa 15 ke kamuwa da ita.

Cutar shuga na cikin ciwo mai cin kudi da yawa a kalla duk wata talaka sai ya kashe dubu shida, mai hali ba zai gaza kashe dubu 20 ba, a wurin kulawa da cutar.

Ciwon nau’i hudu ne akwai nau’i na biyu(Type 2 diabetes) in da ciwon yayi maka lahani sosai ya shafi jikinka da magudanar jininka(chronic condition), sai nau’inta na biyu(Type 1 diabetes) ciwon ya shiga sosai sai dai bai yi lahani kamar na farkon ba, akwai na uku (Prediabetes) shi ne wanda za a aunaka a samu shugan jininka ya hau amma bai kai kamar na biyu ba, nau’i na hudu(Gestational diabetes) shi ko ciwon shuga ne da ake samu ga mata masu juna biyu.

Mutanen da ke iya kamuwa da cutar su ne masu girman jiki da masu hawan jini da tsofafin mutane da wadan da ba su motsa jiki da mutanen da ke cin abinci marar ingancin lafiya.

Masu fama da ciwon suna fama da tsadar magani a Nijeriya abin da ya kamata gwamnati ta shigo ciki domin saukaka masu wahalar sayen magani da suke yi, tun da yanzu an gane kowane abinci suna iya ci, irinsu Gero, Dawa, Masara, Shinkafa da sauransu.

Majalisar dunkin duniya ta ware 14 ga watan Nuwamban kowace shekara ta zama ranar duba  halin da masu ciwon ke ciki domin duba abin da za a iya yi masu na taimako da shawara da wayar da kai.      

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *