Spread the love

Jam’iyar APC ta fada cikin wani sabon rikici bayan da babban daraktan kungiyar gwamnonin jam’iyar APC Salihu Lukuman ya nemi shugabansu na kasa Adams Oshiomhole ya a jiye mukaminsa.

A jawabain da ya fitar jiya Laraba amadadin gwamnonin jam’iyar sun ce shugaban ya yi murabus ya gaggauta kiran taron majalisar zartarwar jam’iyar saboda a warware magangannun da suka ta so a samu wani mutum kamili ya karba daga in da Adams din ya a je.

Gwamnonin sun ce ko shugabansu ya martaba dokokin jam’iya da ta tanadar a matsayinsa na babba gaba daya a jam’iya ya kira taro domin warware matsaloli ko ya aminta da kasawarsa, baya iya jagoranci ya yi murabus kawai.

Lukuman bai bayyana in da gwamnonin APC 18 suka yi taro ba, da wadan da suka halarta da wadanda suka aika wakilai, haka bai bayyana sunayen gwamnonin da ke bukatar shugaban ya ajiye da wadan da ba su gamsu da hakan ba.

Duk kokarin jin ta bakin shugaban gwamnonin APC Sanata Atiku Bagudu gwamnan jihar Kebbi kan wannan maganar ya ci tura.

Abin jira a gani duk wani gwamna da bai fito ya nisanta kansa da abin da Lukuman ya fadi ba yana nufin sun kosa da Oshiomhole, da wuya kuma ya sha.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *