Mahaifiyar yara hudu mai suna Hassana Saleh an samu nasarar kubutar da ita a wani daki da yayanta ya kulle ta a unguwar Rigasa karamar hukumar Igabi jihar Kaduna dake cikin kwaryar birnin jihar.

Hassana yayanta Lawal Saleh ne ya rufe ta cikin daki nan take ci da sha da fitsari da kashi tsawon shekara biyu.

Manema labarai sun samu labarin ne a lokacin da ‘yan sanda suka je wurin suka balle makullin da aka rufe dakin da shi.

Hajiya Rabi Salisu Ibrahim wadda ta assasa gidauniyar tallafi mai suna Arida ce ta kubutar da Hassana ga wannan lahani da yayanta ya yi mata, a dalilinsa na yin haka wai saboda kanwarsa ta nace lalle sai ta koma gidan mijinta shi ne ya sa ya rufe ta.

Ta ce Dangin matar sun tabbatar mijin nata baya son ta kuma har ya sake ta abin da yakai ta ga rudewa. Kan haka shi kuma ya dauki matakin rufe ta a daki don bai da abin da zai iya sai wannan.

Ta ce matar na bukatar a duba lafiyarta don haka take kira ga masu hali su taimaka domin kai ta asibiti

A hidikwatar ‘yan sanda Lawal ya ce ya rufe kanwarsa ne domin ya taimake ta domin bai san abin da zai yi ba, da ya sake ta guduwa za ta yi.

Ya ce ta taba gudu daga baya ta dawo gidansa, in da yake zaune da matansa hudu da ‘ya’ya 41 a Rigasa. ‘Na yi kokari na samar mata magani, amma ita ta nace sai ta koma wajen tsohon mijinta, ta yi wani aure amma ta ki zama domin ita dai gidan tsohon mijinta take son komawa uban ‘ya’yanta.’

Ya ce ya yanke shawarar ya rufe ta cikin daki ne domin ba ya da zarafin da yake iya biyan kudin maganinta, “Ko abin da muke ci yana zame mana matsala gare ni da gidana gaba daya”

Kan zargin ya rufe ta tsawon shekara biyu ya ce ba gaskiya ba ne wata bakwai ne ba shekara biyu ba.

Kan yanayin dakinda aka ajiyeta kuma ya ce kannenta su biyu suna shiga su yi mata wanka su gyara dakin a kallan sau daya a rana. A dukkan unguwarmu an san da labarinta domin ta taba gudu. sai dai muna rokon Allah ya ba ta lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *