Spread the love

Wasu da za su ci gajiyar dubu 10 da gidauniyar Ɗangote ta bayar ga Zawarawa da uwayen marayu da tsoffi mata, akwai zargi mai karfi ba dukkan matan da aka tantance ke karbar kudinsu cikakku ba, ana samun ragin daga wurin jagororinsu.

A binciken da aka yi yanda aka raba kudin a karamar hukumar Dange shuni, a garin Shuni na jihar Sokoto, an gano cewa matan da aka tantance suna komawa gidajensu da 3000 wasu da 5000 mai makon dubu 10 da aka ware a baiwa kowace mace daga cikin matan dubu 23 a kananan hukumomi 23.

Wata tsohuwa a garin Shuni ta ce dubu uku kawai Lami matar Sarkin Gabas na Dabagin Ardo ta bata, matar uban kasa kenan.

A cewar wata Bazawara mai sayar da tafasa matar Sarkin Gabas ta kirani ta tura ni zuwa Amanawa na je na karbo kudin tallafin Dangote bayan na dawo na tafi wajenta ta karbi kudin ta bani dubu uku cikinsu.

Hakimin Shuni Alhaji Sanusi Muhammad ya ƙaryata zargin ya ce ba gaskiya ba ne ba wata mace da ba a bata kuɗinta cikakku ba.

Ya ce sai dai shi yana da mutum 20 da ya zaɓo a ba su tallafin sai aka neme shi da ya kawo 17, gudun rikici ne suka ce a raba kuɗin yanda kowa zai samu cikinsu.

Sarkin Gabas Abubakar Ahmad ya ce ba zai yi magana ba don baya jin daɗi ɗiyarsa ta rasu.

Bayar da kuɗin nan akwai ƙorafe-ƙorafe da dama da mutane ke yi wasu su ce an sauya sunansu da aka samu labarin kuɗi za a bayar. Wasu raba daidai aka yi musu.

Managarciya ta so ta ji ta bakin Shugaban hukumar Zakka da Waƙafi Malam Muhammad Lawal Maidoki don sanin matakin da za su ɗauka yanda kwaliya za ta biyan kuɗin sabulu, wanda gidauniyar ɗangote ta tantance a ba ta kuɗinta gaba ɗaya, sai dai baya ƙasar yana cikin tawagar gwamnan Sokoto Alhaji Aminu Waziri Tambuwal sun je Amerika a haɗuwar da gwamnan zai yi da Bill Gates da Ɗangote.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *