Spread the love

Zauren majalisar dattijai na tarayyar Nijeriya ya ga laifin jami’an kamfanin NNPC da hukumar kula bututun mai ta Nijeriya kan zargin suna hada baki da masu lalata bututun(Pipeline) don a kawo wa kasa cikas.

Wannan ya biyo bayan duba rahoton da kwamitin wuccin gadin da majalisar dattijan ta kafa domin ya binciki dalilin lalacear bututun mai a jihhar Lagas da Rivers.

Shugaban majalisar dattijan Ahmad Lawan ya yi kira da abincike dalilin lalacewar bututun a jihar Rivers kwana biyu bayan ya fashe, wasu jami’an kamfanin suna da masaniyar bututun dake Komkom yana yoyo amma suka ki daukar mataki.

Lawan ya ce yakamata a kama wadan nan jami’an kuma a hukunta su.

Majalisa ta umarci kamfanin NNPC ya mayar da kudin da suka ce sun kashe a wurin gyaran bututun Komkom, miliyan 382 ne suka ce sun batar a wurin yakar wuta lokacin aikin, su mayar da su a asusun gwamnatin tarayya.

Majalisa ta gayyaci shugaban domin yin karin bayani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *