Spread the love

‘Yan majalisar wakillan Nijeriya sun yi kira ga hukumar fasa kwabri da aka fi sani da Kwastam da su janye haramcin sayar da man fetur a gidajen mai dake garuruwa na kusa da iyakokin Nijeriya matukar bai wuce kilo mita 20 ga boda ba.

Bayan amincewa da kudirin da dan majalisar wakillan tarayyar Nijeriya Sada Soli Jibiya(APC Katsina) ya gabatar in da ya bayyana hadarin dakatarwar ga mutanen da ke rayuwa a kusa ga iyakokin.

Jibiya ya ce dakatarwar za ta kara matsin rayuwa ga mutanen da ke zaune a kusa ga iyakokin. Kuma wannan hukuncin na kwastam warwara ne ga dokokin da suka samar da dokar kafa hukumar Kwastam.

Ya ce nuna karfin iko ga hukumar kwastam na bayar da umarni sabawa dokarsu ne, wadda aka yi wa gyaran fuska.

Sada Jibiya wanda mazabarsa na cikin wuraren da suka yi iyaka tsakanin Nijeriya da Nijar ya ce baya shakku an karawa mutanen da ke kusa boda wahala bayan wadda suke ciki ta rufe boda, suna ji a jiki fiye da kowa a kasar ann.

Ya nuna damuwarsa sosai mutanensa na bukatar man kamar yadda kowa ke bukatarsa don kowa ya san yanda aka mayar da komai sai da man fetur a Nijeriya.

Ya ce akwai bukata hukumar DPR ta ce wani abu kan wannan lamari

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *