Spread the love

Wani kamfanin harkar sufuri dake jihar Kano ya yi ƙarar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da sakataren gwamnatin tarayya kan zargin ƙara wa’adin jagorancin tafiyar da hukumar alhazai ta ƙasa da aka yi wa shugaban Abdullahi Mukhtar Muhammad.

Mai ƙara Malam Mas’ud Mu’azu ya roƙi babbar kotun tarayya dake Abuja ta ayyana ƙarin wa’adin abin da ya saɓawa doka baya cikin tsarin dokokin ƙasa a ƙarawa shugaban hukumar wa’adi.

Haka kuma shari’ar an sanya babban lauyan ƙasa da hukumar alhazzan.

Ƙarar wadda lauya Ibrahim Alhassan ya shigar amadadin mai ƙara ya roƙi kotu ta ɗauki abin da shugan ƙasa ya yi saɓawa sashe na 171 a tsarin kundin dokokin ƙasa na shekarar 1999 da shashe na 5 a daftarin tsarin hukumar alhazzai ta ƙasa da aka ƙirƙira a 2006.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *